Trump: Martani na tafe kan harin Iran a Riyadh
March 3, 2026
Kasar Iran ta kaddamar da jerin hare-haren makamai masu linzami da jiragen yaki marasa matuka a daren Litinin wayewar garin Talata, inda ta kai hari kan wasu kasashen yankin Gulfda suka hada da Saudiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa, Qatar da kuma Isra'ila.
Karin bayani: Iran ta zafafa hare hare kan Isra'ila da sansanonin Amurka
Hare-haren sun fara ne da tala-tainin dare, yayin da sojojin Isra'ila suka ce suna kokarin kakkabe makamai da aka harba zuwa wurare da dama ciki har da birnin Kudus. Hadaddiyar Daular Larabawa ta ce ta fuskanci wasu makamai masu linzami, yayin da Qatar ta sanar da kakkabe makamai guda biyu da safiyar Talata.
A Saudiyya kuwa, an ji karar fashewar abubuwa a birnin Riyadh, inda ma'aikatar tsaro ta kasar ta ce ta kakkabe makamai takwas, yayin da Iran din ta kai hari ofishin jakadancin Amurka da ke Riyadh.
Sai dai shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce Amurka za ta mayar da martani nan ba da jimawa ba.