Trump na brazanar rufe sararin samaniyar Venezuela
November 30, 2025
Shugaban Amurka Donald Trump, ya tsananta barazanarsa a kan Venezuela tare da gargadin rufe ilahirin sararin samaniyar kasar, lamarin da ke kara nuna fargabar daukar matakin soji.
Trump ya wallafa a shafinsa na sada zumunta Truth cewa, " Ina jan hankalin kamfanonin jiragen sama da matuka jirage da dillalan kwaya da masu safarar mutane, ku lura, za akwai yiwuwar killace sararin samaniyar Venezuela a kowane lokaci."
Sai dai Trump bai yi wani karin haske ba, amma munanan hare-haren Amurka kan jiragen ruwa da ake zargi na masu safarar kwayoyi, alamar Washingtong na iya kai farmaki a Venezuela.
Gwamnatin Shugaba Maduro a Caracas, wacce ke kallon yawan sojojin Amurka a yankin na Caribbean a matsayin wani yunkuri na hambarar da shugaba Nicolas Maduro, kasar ta kuma yi Allah wadai da gargadin na Trump da cewa "barazana ce ta 'yan mulkin mallaka."