Trump na duba yiwuwar kawo karshen yakin Iran
March 21, 2026
Talla
A wani sakon da ya wallafa a shafin sada zumunta na Truth Socials, Trump ya ce sun kusa cimma muradunsu a yakin da suke yi da Iran, don haka suna duba yiwuwar kawo karshen ayyukan sojoji a yankin Gabas ta Tsakiya kan kasar Iran.
Kazalika Trump ya ce alhakin kula da ayyukan dake gudana a mashigin ruwa na Hormuz zai koma ga kasashen dake amfana da shi.
Farashin mai a kasuwannin duniya na ci gaba da tashin gouron zabi tun bayan rufe mashigin Hormuz da kasar Iran ta yi.
A baya dai shugaban na Amurka ya yi kira ga kasashen yamma don goya masa baya na kare mashigin, kiran da kasashe irinsu Jamus da Burtaniya da Faransa suka juya wa baya, matakin da ya ce ka iya yin barazana ga kawancen NATO.
Karin Bayani: