Trump na karbar bakoncin Firaministan Italiya
July 30, 2018Shugaban Amirka Donald Trump na karbar bakoncin Firaministan Italiya Giuseppe Conte a fadar White House, inda ake sa ran shugabannin biyu za su tattauna kan huldar dangantaku tsakanin kasashensu.
Wannan shi ne karo na farko da Firaministan na Italiya ya kai ziyara a fadar White House. Sau da yawa an ji Trump na nuna kamanceceniya tsakaninshi da Firaministan na Italiya musamman dangane da batun bakin haure.
A ganawa da manema labarai kafin sun kebe zauren tattaunawa, Trump cewa ya yi.
"Ina godiya da zuwanka nan. Mun zama abokai tun a tarukan G7. Na amince kana tafiyar da aiki mai kyau musamman dangane da masu kaura da bakin haure. Italiya na daukar matakan da suka dace a kan iyakokinta, matakin da wasu daidaikun kasashe suka riga suka dauka."
Taron dai na zuwa ne bayan da a ranar Lahadi Trump ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa a shirye yake ya rufe dukkan ma'aikatun gwamnati idan 'yan jam'iyaar Demokrats suka ki jefa kuri'a kan kare iyakokin Amirka ciki har da batun gina katanga tsakaninta da Mexiko.