1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump na neman a kawo karshen yakin Ukraine

December 8, 2024

Zababben shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya yi kira da a gaggauta cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Ukraine.

Shugaba Donald Trump na Amurka da Volodmyr Zelenkyy na Ukraine
Shugaba Donald Trump na Amurka da Volodmyr Zelenkyy na Ukraine Hoto: Ludovic Marin/AFP via Getty Images

Zababben shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya kira a tsagaita bude wuta a Ukraine bayan da ya gana da Shugaba Volodmyr Zelensky na Ukraine da kuma Emmanuel Macron na Faransa a birnin Paris.

Shugaban mai jiran gado ya ce, Ukraine na son samar da wata yarjejeniya da za ta kawo karshen mamayar da Rasha ta kaddamar mata. Shugaba Trump ya kara da cewa, ana asarar rayuka da dama a yakin da bai kamata tun da fari a yi shi ba, yana mai yin kira ga Shugaba Vladmir Putin na Rasha da ya kawo karshen yakin da aka kwashe kusan shekaru uku ana gwabzawa.

Karin bayani: Shugaban Ukraine Zelensky ya nemi a sulhunta su da Rasha

A yayin da take mayar da martani, Rasha ta ce kofar ta a bude take domin a hau kan teburin tattaunawa. Fadar gwamnatin Kremli dai ta dade tana ikrarin cewa, za a cimma yarjejeniyar zaman lafiya ne kadai bisa yarjejeniyar birnin Santabul a shekarar 2022, sai dai Rasha ta zargi Ukraine da yin watsi da wannan yarjejeniyar.