1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump na neman dage zaben shugaban Amirka

Mouhamadou Awal Balarabe
July 30, 2020

Shugaba Trump ya dogara a kan karuwar da ake samu na aikewa da kuri'a ta gidan waya wajen kira da a jinkirta zaben watan Nuwamba, inda ya ce wannan zai iya haifar da magudi da sakamakon zabe maras inganci.

US-Präsident Donald Trump
Hoto: picture-alliance/AP Photo/E. Vucci

A karon farko, Shugaban Amirka Donald Trump ya nuna yiwuwar dage zaben shugaban kasa na 3 ga Nuwamba sakamakon yaduwar da annobar corona ke yi a kasar tamkar wutar daji. Cikin wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Tweeter, Trump ya ce zaben na fuskantar barazanar "magudi sakamakon zabe mafi karancin inganci da za a gudanar" a tarihin kasar Amirka, lamarin da ya ce zai iya zama "babban abin kunya ga kasar" idan aka samu karuwar yin zabe ta hanyar aikewa da wasiku a gidan waya. Sai dai shugaban bai bayar da wata kwakkwarar hujja game da tsoron da ya ji na magudi da kuste a zaben ba. 

Ana ganin cewa Trump zai fuskanci cikas wajen dage zaben saboda doka ta riga ta kayyade lokacin da ya kamata a gudanar da shi. A halin yanzu dai, kididdigar jin ra'ayin jama'a ta nuna cewa Donald Trump na bayan abokin hamayyarsa Joe Biden na jam'iyyar Democrats a yawan wadanda za su kada masa kuri'a .