1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Trump na neman taimakon kasashe don kare mashigin Hormuz

March 15, 2026

Iran na ci gaba da kai hare-haren ramuwar gayya kan kasashen yankin Gulf tare da yin barazanar lalata muradun Amurka muddin Washington ta yi kuskuren lalata mata cibiyar mai ta tsibirin Kharg.

Persischer Golf | US-Kriegsschiff USS Boxer auf Patrouille
Hoto: Cappello/Fotogramma/ROPI/picture alliance

Shugaban Amurka Donald Trump ya bukaci sauran kasashen duniya da su aike da jiragen ruwan yaki domin tabbatar da tsaron mashigin Hormuz wanda Iran ta yi barazanar kawo wa cikas saboda yakin da take gwabzawa da kawancen Amurka da Isra'ila.

Trump ya ce sojojin Amurka sun "lalata kwata-kwata" garkuwar sojojin Iran a tsibirin Kharg, dake a tazarar kilomita 30 daga gabar Tekun Fasha, wadda ke zama tashar fitar da danyen mai mafi girma ga Teheran.

Shugaban na Amurka ya kara da cewa yana fata kasashen Chaina da Faransa da Japan da Koriya ta Kudu da Birtaniya da sauran su za su gaggauta aikewa da jiragen ruwa zuwa yankin don tabbatar da cewa Iran da aka riga aka gama da ita ba ta hana jirage wucewa ba.

Rahotannin na cewa an jiyo karar fashewar wasu abubuwa kusan 15 a tsibirin Kharg a jiya Asabar, sai dai kamfanin dillancin labaran Iran na Fars ya ruwaito cewa ba a lalata komai daga cikin tsarin samar da man kasar ba.

Hoto: Hossein Beris/Middle East Images/AFP/Getty Images

Bazanar Iran ga Netenyahu

Dakarun kare juyin juya halin Musuluncin Iran sun lashi takobin "farauta da kuma kashe" firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, a daidai lokacin da aka shiga rana ta 16 da barkewar yaki a tsakanin Jamhuriyar Musuluncin Iran da kawancen Isra'ila da Amurka.

A wani sako da suka wallafa a shafinsu na Intanet na Sepah News, dakarun juyin juya halin sun ce idan har mista Netanyahu da suka bayyana a matsayin ''dan kisan gilla mai kashe yara'' na raye to ba shakka za su ci gaba da farautar sa domin ya girbi abin da ya shuka.

A daidai wannan lokaci Iran na ci gaba da kai hare-haren ramuwar gayya kan kasashen yankin Gulf, inda a wannan safiya ta Lahadi aka jiyo karar fashewar abubuwa masu karfi a Manama fadar gwamnatin Bahrain kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Hakazalika ma'aikatar tsaron Saudiyya ta ce ta lalata wasu jiragen yaki maras matuka guda 10 da suka nufi Riyadh babban birnin kasar, sai dai Iran ta ce ba tada alaka da wannan hari.