Trump na shan suka kan yarjejeniyar Paris
June 2, 2017Talla
Donald Trump ya ce ba zai amince da duk wani mataki da zai musgunawa 'yan kasar sa ba, inda yake ganin tsarin da zai haramta wa kamfanoni fidda iskar gas, ka iya jefa Amirkawa da dama cikin rashin aikin yi. Kasar Amirka ce ta biyu a kasashe mafi girman masana'antu da ke fidda iskar guba a duniya baya ga kasar China.
Sai dai matakin na Trump ya zama mai harshen damo da ke nuna alamun yiwuwar sake waiwayar yarjejejniyar ko ma ya sake neman kulla wata sabuwa ta daban anan gaba. Amma kasashen China, Rasha, Faransa, Jamus da Italiya, na cikin sauran kasashen duniya da suka soki lamarin hada da toshe bukatar Trump na sake shiga yarjejeniyar a nan gaba. Inda kungiyar Tarayyar Turai ke ganin kasar China na dab da maye gurbin Amirka.