1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Trump na shirin tura karin sojoji 5,000 Poland

May 22, 2026

Matakin na shugaban Amurka na zuwa a daidai lokacin da sabani ke kara fitowa fili a tsakaninsa da shugaban gwamnatin Jamus kan yakin Iran.

Amurka na shirin tura karin sojoji 5,000 zuwa Poland
Amurka na shirin tura karin sojoji 5,000 zuwa PolandHoto: Nicolas Armer/dpa/picture alliance

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa yana shirin tura karin sojoji 5,000 zuwa kasar Poland, saboda kyakyawar alaka da ke tsakaninsa da sabon shugaban kasar mai ra'ayin kishin kasa Karol Nawroki.

Sanarwar ta Trump na zuwa ne kwanaki biyu bayan da ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta ce za ta rage yawan rundunonin sojinta da ke jibge a nahiyar Turai daga hudu zuwa uku.

Amurka ta janye sojinta daga Jamus bayan kin yakin Iran

Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da sabani ke kara fitowa fili a tsakanin shugaban Amurka Donald Trump da shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz kan matakin Berlin na yin tir da yakin Iran.

A baya dai wasu kalamai da shugaban gwamnatin Jamus ya furta kan cewa ''Iran ta tozarta Amurka'' sun fusata Trump, lamarin da ya kai Washington ga sanar da shirin janye sojojinta 5,000 daga Jamus a farkon wannan wata na Mayu.