1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump: Don ni ake binciken harin Capitol

Abdul-raheem Hassan
July 18, 2023

Tsohon Shugaban Amirka Donald Trump, ya ce yana sa ran za a tuhume shi kan harin da aka kai majalisar dokokin kasar a ranar 6 ga watan Janairun 2021.

Tsohon Shugaban Amirka Donald Trump
Hoto: EVELYN HOCKSTEIN/REUTERS

Trump mai shekaru 77 a duniya,yana shirin sake takarar shugabancin Amirka a jam'iyyar Republican a shekarar 2024, sai dai yanzu haka Trump yana fuskantar shari'a a kan zargin aikata laifuka da lauya na musamman Jack Smith yake masa na karkatar da wasu muhimman takardun sirri na gwamnati bayan barinsa fadar White House.

Trump ya ce ya samu wasika daga Smith a ranar 16 ga watan Yulin 2023 yana mai cewa "Ni ne makasudin binciken da aka yi a ranar 6 ga Janairu, 2021" a lokacin da magoya bayan Trump suka kutsa cikin zauren majalisa a wani yunkuri na hana ba wa Shugaba Joe Biden takardar shaidar cin zaben a 2020.