1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Trump ya bai wa Hamas wa'adin sakin Isra'ilawa da ke Gaza

February 11, 2025

Kalaman na Donald Trump sun biyo bayan sanarwar dakatar da sakin Isra'ilawa ne da Hamas ta yi a ranar Litinin.

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald TrumpHoto: Kyodo/picture alliance

Shugaban Amurka Donald Trump ya bai wa kungiyar Hamas ta zirin Gaza wa'adin sakin dukkan  Isra'ilawa da suka saura a hannunta ko kuma ta fuskanci mummunan al'amari.

Trump ya yi kalaman nasa ne biyo bayan sanar da dakatar da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma da Hamas ta sanar a ranar Litinin.

Mista Trump ya ce daga yanzu zuwa karfe sha biyu na ranar Asabar idan ba a saki dukkan fursunonin yakin da ke hannun Hamas ba to za a fada mummunan yanayi.

Netanyahu zai gana da Trump kan yakin Gaza

Ko da yake Trump ya kara da cewa maganar ta kashin kansa ce, saboda daukar mataki na wuyan Isra'ila wacce ya ce matakin nata ka iya zama daban da kalamansa.

Gaza: Trump ya bukaci Masar da Jordan su karbi Falasdinawa

Dama an tsara sako karin wasu Isra'ilawa uku a ranar Asabar mai zuwa kafun sanarwar ta Hamas inda ta ce Isra'ila ta karya ka'idar yarjejeniyar.