1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump ya bayyana nasarorin gwamnatinsa

February 25, 2026

Shugaban Amurka Donald Trump, ya gabatar da jawabin halin da kasa ke ciki. Sai dai yanzu kalubalen da ke gabansa shi ne yadda zai tabbatar da sakon nasa ya yi tasiri ga jama'a.

Jawabin Trump a majalisar dokoki
Jawabin Trump a majalisar dokokiHoto: Jessica Koscielniak/AP Photo/picture alliance

A jawabin da ya gabatar ranar 24 ga watan Fabrairun 2026, Trump ya bayyana irin farin ciki da nasarorin da gwamnatinsa ta samu a wa'adinsa na biyu da bai dade da farawa ba.

Ya yi ikirarin farfado da tattalin arzikin cikin gida, tare da jaddada cewa Amurka na taka rawa wajen tsara fasalin harkokin waje na kasashen duniya.

A karshen mako, Trump zai kai ziyara jihar Texas, domin gwada yadda sakon nasa zai karbu gabanin zaben tsakiyar wa'adi. Fadar White House na kokarin yada wannan sako ga karin masu zabe, a daidai lokacin da rahotanni ke nuna cewa da dama daga cikinsu ba su gamsu da yadda yake tafiyar da mulki ba, yayin da a wani bangaren kuma rikicin Gabas ta Tsakiya ke barazanar dauke hankali daga manufofinsa na cikin gida.