Me zai faru a tattaunawar rikicin Gaza a Masar?
October 6, 2025
Shugaba Trump ya bayyana cewa mataki na farko na shirin samar da zaman lafiya a Gaza wanda ya hada da musayar fursunoni da tsagaita wuta na wucin gadi, zai iya kammaluwa cikin kwanaki kadan idan bangarorin suka amince da tsarin da ya gabatar.
Me ke faruwa a Alkahira?
Masar ce ke karbar bakwancin wannan muhimmin taro, inda wakilan kungiyar Hamas da Isra’ila ke halarta tare da jami’an Amurka. Babban abin da ake so a cimma a yanzu su ne:
-
A saki wasu fursunonin Isra’ila da ke hannun Hamas
-
Isra'ila ta sako Falasdinawa da ke kurkuku
-
sannan a sami tsagaita wuta domin a shigar da kayan agaji da taimakon jin kai cikin Gaza.
Muhimman abubuwa a shirin zaman lafiya da Trump ya gabatar
Rahotanni daga fadar White House da kafafen watsa labarai sun bayyana cewa shirin da Amurka ta gabatar yana da matakai guda uku, kuma ya kunshi abubuwa kamar haka:
-
Sakin fursunoni da tsagaita wuta a matakin farko, musamman a yankunan da ake kai hare-hare.
-
Janyewar sojojin Isra’ila daga wasu wurare domin bayar da damar shigar da agaji.
-
Kafa gwamnatin rikon kwarya a Gaza wacce za ta hada da kwararru daga kasashen waje da Larabawa, ba ta Hamas ko Isra’ila kai tsaye ba.
-
Kwance damarar yaki wa kungiyoyin Hamas ko wasu kungiyoyi masu daukar makamai.
Trump ya ce wannan tsarin “na daki-daki ” ne, domin a fara kare rayuka da sake dawo da fursunonin da ke tsare, sannan daga baya a tattauna batun siyasa da gyaran Gaza.
Duk da tattaunawar da ake yi, har yanzu ana samun hare-hare da mutuwar fararen hula a Gaza. Rahotanni daga kungiyoyin agaji na cewa mutane na fama da karancin ruwan sha da abinci da magunguna. Wannan shi ne dalilin da yasa Amurka ke matsa lamba a yi saurin cimma matsaya.
Matsayin bangarorin da ke shiga tattaunawar
-
Isra’ila: Ta nuna shirin tattaunawa, amma tana son tabbacin kasarta ba za ta fuskanci barazanar tsaro ba. Wasu ’yan siyasa a Isra’ila ba sa son a bai wa Hamas damar ci gaba da iko daGaza.
-
Hamas: Ta nuna bukatar ganin an saki fursunoni da kuma samar da tsaro ga jama’ar Gaza, amma tana da ra’ayoyi masu sabani a cikin shugabancinta kan batun mallakar makamai.
-
Masar da kasashen Larabawa: Su ne ke shiga tsakani domin ganin an samu sulhu, musamman domin kare yankin daga tashin hankali.
-
Amurka: Donald Trump da tawagarsa suna matsa lamba sosai domin a cimma yarjejeniyar cikin gaggawa, suna cewa Washington za ta kasance kan gaba a aiwatar da shirin.
Matsalolin da za a iya fuskanta
-
Matakin da Isra’ila za ta dauka game da janyewar sojojinta.
-
Wanda zai gudanar da gwamnatin rikon kwarya a Gaza.
-
Batun ajiye makaman Hamas – wane ne zai kula da tsaron yankin Gaza bayan tsagaita wuta.
-
Tsarin tabbatar da musayar fursunoni cikin aminci.
Kasashen duniya da dama sun yi maraba da tattaunawar, suna kira da a yi saurin cimma yarjejeniya mai dorewa. Sai dai wasu masana sun yi gargadin cewa idan ba a kafa tsari na dindindin ba, wannan tsagaita wuta na iya zama na jeka na yi ka kawai.
Me za a sa ido a kai cikin kwanaki masu zuwa?
-
Shin za a iya cimma tsarin musayar fursunoni cikin gaggawa?
-
Shin majalisar ministocin Isra’ila za ta amince da shirin gaba daya?
-
Shin Hamas za ta amince da tsarin gwamnati na wucin gadi a Gaza?
-
Kuma shin za a samu izinin shigr da kayan agaji a Gaza cikin lumana?
Umarnin Trump na cewa “a gaggauta” tattaunawar, na nuna yadda Amurka ke son ganin an kawo karshen tashin hankali cikin hanzari. Amma nasarar wannan shiri zai dogara ne da yadda bangarorin biyu za su yarda da juna, da kuma yadda za a tabbatar da tsaro da taimakon jin kai ga al’ummar Gaza.