Trump ya bukaci tattaunawa da Kim Jong Ung
January 10, 2018Talla
Fadar shugaban kasar Amirka ta White House ta ce Shugaba Trump ya bayyana matakin bude kofar shiga tattaunawa da shugaban kasar koriya ta Arewa a yayin zantawa da shugaban Koriya ta Kudu Moon Jae-In ta wayar tarho.
Sabon babin neman dinke barakra da ke tsakanin Amirka da Koriya ta Arewar ta biyo bayan tasirin sabunta dangantaka tsakanin shugaba Kim Jong Ung na Koriya ta Arewa da Koriya ta Kudu da suka shafe shekaru biyu suna wa juna kallon hadirin kaji.
Shugaban kasar koriya ta Kudu Moon Jae-In ya ce yana cike da fatan tattaunawarsu da Kim Jong Un zai bada damar tattaunawa a kan kera makaman kare dangi da Koriya ta Arewa ke sa-in-sa da sauran kasashen duniya.