Trump ya yi barazanar karawa Canada haraji a kan China
January 24, 2026
Talla
Dangantaka tsakanin Amurka da makwabciyarta ta yi tsami tun bayan komawar Trump ga karagar mulkin kasar inda aka yi ta cece-ku-ce kan harkokin kasuwanci da firaministan Canada Mark Carney ya yi Allah wadai da sabbin matakan Amurka musamman ma na kasuwanci a kasarsa.
A wata ziyara da ya kai Beijing a makon da ya gabata, Carney ya yaba da sabuwar dangantakar kasashen biyu wanda ta haifar da yarjejeniyar cinikayya ta farko a tsawon tarihi da za ta rage zafin harajin Amurka a kasar.
Trump ya sha alwashin daukar tsauraran matakai idan wannan yarjejeniyar ta kullu. A wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Truth Socials, Trump ya ce idan Canada na shirin zama inda China za ta jibge kayayyakinta don shigar da su Amurka to ta yi kuskure.