1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Yakin Iran ya kusa kawo karshe - Trump

March 10, 2026

Shugaba Trump ya saka duniya cikin rudani da rashin tabbas bayan da ya furta cewa yakin Iran ya kusa kawo karshe amma ba tare da ya sanar da lokaci ba.

Trump na yi wa taron jam'iyyar Republicain jawabi kan burinsa a yakin Iran
Trump na yi wa taron jam'iyyar Republicain jawabi kan burinsa a yakin IranHoto: Kevin Lamarque/Reuters

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa yakin Iran zai kawo karshe nan ba da dadewa ba, yana mai ishara da cewa an cimma burin da ake so cikin sauri sabanin yadda tun da farko ya yi hasashen cewa yakin zai dauki dagon lokacin har zuwa mako hudu zuwa biyar.

Na rufe kofar tattaunawa da Iran - Trump

A lokacin da yake wannan furuci a yayin wani taron manema labarai a birnin Miami, shugaba Trump ya ce idan aka sake shiga wani yakin a nan gaba Iran za ta ji a jikinta fiye da abin da ta gani a yanzu.

Shugaban na Amurka ya kuma yi barazanar cewa Iran za ta dandana kudarta muddin ta ci gaba da yin garkuwa da duniya ta hanyar toshe mashigin Hormuz, wanda kashi  daya bisa biyar na mai da isakar gaz na duniya ke wucewa ta cikinsa.

Trump na son kasar Iran ta mika kai bori ya hau

Sai shugaban hukumar tsaron Iran Ali Larijani ya yi gargadin cewa mashigin na Hormuz zai ci gaba da kasasncewa a rufe matukar yakin ya dore, lamarin da ya kara saka duniya cikin rudani da rashin tabbas.