Trump ya dakatar da wakilansa halartar taron sulhu da Iran
April 25, 2026
Shugaba Donald Trump na Amurka ya dakatar da wakilansa daga halartar taron sulhu da Iran na birnin Islamabad, sa'o'i kalilan gabanin bulaguron sirikinsa Jared Kushner da kuma wakilinsa na musamman a Gabas ta Tsakiya Steve Witkoff zuwa Pakistan.
Mr Trump ne da kansa ya fitar da wannan sanarwa, yayin tattaunawa da kafar yada labarai ta Axios ta wayar tarho, sannan kuma daga bisani ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na Truth social.
karin bayani: Tsagaita wuta a Lebanon na tangal-tangal
To sai dai shugaban ya ce soke bulaguron wakilan na sa, baya nufin Amurka za ta ci gaba da yaki da Iran, to sai dai ya ce kofarsa a bude take, matukar Iran na bukatar kiransa ta waya, don tattaunawar kawo karshen yakin baki-daya.
Gabanin jin wannan sanarwa ta shugaba Trump, ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi, ya bar birnin Islamabad na Pakistan a wannan Asabar, ba tare da yin tozali da wakilan Amurka ba, a kokarin da bangarorin biyu ke yi na ganawa da juna, kan yarjejeniyar dakatar da yakin da suke gwabzawa.
karin bayani: Italiya ta bijire tayin Amurka na maye Iran a kofin duniya
Ministan harkokin wajen Pakistan, kuma mataimakin firaminista Ishaq Dar, ya ce gabanin barin Pakistan, Mr Araghchi ya samu ganawa da firaministan kasar Shehbaz Sharif da kuma babban hafsan sojin kasar Field Marshal Asim Munir, inda suka shafe tsawon sa'o'i biyu suna tattaunawa.
Iran ta sha nanata cewa babu ta yadda za a yi ta aminta da alkawuran da Amurka ke mata, la'akari da yadda ta far mata da yaki haka kwatsam rana tsaka, bisa hadin gwiwar Isra'ila, a daidai lokacin da ake tsaka da tattaunawar sulhu, kan shirinta na mallakar makamin nukiliya.
Karin bayani:Trump ya ce zuwan sarki Charles Amurka zai dinke baraka
A ranar Juma'a aka jiyo fadar mulkin Amurka ta White House na shelanta shirin shugaba Donald Trump, na aikewa da sirikinsa Jared Kushner da kuma wakilinsa na musamman a Gabas ta Tsakiya Steve Witkoff zuwa Pakistan, domin ci gaba da tattaunawar lalubo hanyar dakatar da yakin na Iran.