1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Trump ya daukaka kara zuwa kotun koli

Abdullahi Tanko Bala
January 4, 2024

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya daukaka kara zuwa kotun koli kan hukuncin kotun Jihar Colorado da ta haramta masa tsayawa takara a zaben 2024

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump
Tsohon shugaban Amurka Donald Trump Hoto: Kamil Krzaczynski/AFP/Getty Images

Jihar Colorado ita ce ta farko da ta yanke hukuncin haramta wa   Trumptakara bisa tuhumarsa  da tunzura afka wa majalisar dokokin Amurka a ranar 6 ga watan Janairun 2021.

Trump wanda ke kan gaba a  cikin 'yan takarar neman shugabancin kasar Amurka na 2024 a Jam'iyyar republican yana bukatar kotun kolin ta sake duba hukuncin.

Karin Bayani: Trump: Ni ake hari a binciken Capitol

Manazarta dai na ganin karar za ta jefa kotun kolin cikin wadi mai sarkakakiya na siyasa.

Uku daga cikin alkalan kotun dai Trump ne ya nada su a lokacin da ya ke shugaban kasa.