1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Trump ya fusata game da ta'asar da ake yi a Sudan

November 20, 2025

Amurka na shirin yin aiki tare da kawayenta na yankin Gabas ta Tsakiya domin kawo rikicin Sudan wanda ya haddasa matsalar jin kai mafi muni a duniya a cewar MDD.

USA Washington D.C. 2025 | Donald Trump kehrt aus Florida ins Weiße Haus zurück
Hoto: Pool/ABACA/IMAGO

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya kadu matuka da irin ta'asar da ake yi a Sudan, kasar da yaki na sama da shakaru biyu ya daidaita, yayin da yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed ben Salmane ya roke shi da ya shiga lamarin ko an kawo karshen zubar da jini.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Shugaba Trump ya ce zai yi aiki kafada da kafada da kasashen Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa da Masar da kuma sauran kawayen Amurka na yankin Gabas ta Tsakiya domin kawo karshen ta'asar da ake tabkawa a Sudan.

Tuni dai gwamnatin rikon kwaryar Sudan karkashin shugaban mulkin soji Abdel Fattah al-Burhane ta mayar da martani tana mai cewa a shirye take ta hada kai da Washington da Riyadh domin duba wannan lamari.

Dama dai a can baya Amurka ta yi yunkurin shiga tsakani a rikicin na Sudan da ya barke yau sama da shekaru biyu, wanda MDD ta bayyana cewa ya haddasa matsalar jin kai mafi muni a duniya.