Trump ya gabatar da jawabi a gaban majalisun kasar
February 25, 2026
Jawabin na Trump na zama irinsa na farko mafi tsawo cikin shekaru 62, inda Trump din ya shafe kusan sa'o'i biyu yana bayani a gaban majalisun dokokin Amurka.
To sai dai bisa ga dukkan alamu shugaban da jam'iyyarsa ta Republican suna cikin tsaka mai wuya, inda kuri'ar jin ra'ayoyin al'umma ta nuna cewa galibin Amurkawa ba su amince da yadda Trump ya tafiyar da harkokin gwamnati a shekarar farko da ya hau kan karagar mulki ba.
Shugaban dan jam'iyyar Republican mai shekaru 79, yana fatan zai iya gamsar da Amurkawa masu shakkun cewa manufofinsa sun inganta rayuwarsu tare da tabbatar da cewa tattalin arzikin Amurka ya inganta kuma su zabe shi a zaben tsakiyar wa'adi dake tafe a karshen wannan shekarar.
Trump ya ce bayan shekara guda kawai gwamnatinsa ta samu sauyi da ba a taba ganin irinsa ba. Jawabin nasa na zuwa ne a dai dai lokacin da jiragen yakin Amurka guda biyu ke shirin fadawa yaki a yankin Gabas ta Tsakiya, a daidai lokacin da ake fama da takun-saka da Iran kan shirinta na nukiliya.
Karin bayani:Trump ya yi karin kudin fito daga kashi 10% zuwa 15%