1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump ya godewa Kim Jong Un kan fursunoni

Abdullahi Tanko Bala
May 10, 2018

Trump ya karbi tsoffin fursunoni uku 'yan Amirka wadanda Koriya ta Arewa ta sako daga gidan yari a wani mataki na kyautata dangantakar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu.

USA Donald Trump Nordkorea lässt Amerikaner frei
Hoto: Reuters/J. Bourg

Shugaban Amirka Donald Trump ya yi wa fursunoni uku 'yan Amirka wadanda Koriya ta Arewa ta sako barka bayan da suka sauka a wani sansanin sojin sama a Washington.  

Koriya ta Arewa ta sako mutanen uku ne kwana daya gabanin lokacin da ake sa ran za ta sako su, abin da fadar Amirka ta White House ta baiyana a matsayin kyakkyawar kudiri na ganawar da ake shirin yi tsakanin Trump da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un.

Sakin mutanen uku ya zo ne a daidai lokacin da sakataren harkokin wajen Amirka Mike Pompeo ya kai ziyara kasar domin kammala shirin ganawar shugabannin kasashen biyu da ake shirin za a yi a Singapore a karshen wannan watan ko kuma farkon watan Juni.

Koriya ta Arewa ta zargi mutanen ne da aikin leken asiri.