1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump ya goyi bayan Isra'ila bayan sukar Rasha a taron MDD

September 23, 2025

Shugaban na Amurka ya shafe kusan sa'a daya yana jawabi kan sauyin yanayi da sukar MDD da kuma Turai.

Trump ya ce yana son abokan hulda na Amurka su dauki irin wadannan matakan domin matsa lamba ga Putin.
Trump ya ce yana son abokan hulda na Amurka su dauki irin wadannan matakan domin matsa lamba ga Putin.Hoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya gargadi Rasha inda ya ce yana shirye ya kakaba mata manyan takunkuman karya tattalin arziki idan ba ta yi aiki domin kawo karshen yakin Ukraine ba.

Shugaban ya kuma yi fatali da batun kafa kasar Falasdinu a jawabin da ya gabatar a zauren babban taron Majalisar Dinkin Duniya da ke gudana a birnin New York na Amurka a wannan makon.

Shugabannin duniya sun fara jawabi a taron MDD na 80

Har ila yau, a jawabin nasa Trump ya soki Tarayyar Turai kan manufofinta na bakin haure da 'yan gudun hijira.

Ya ce shugabannin kasashe su daina kokarin yakar sauyin yanayi, inda ya kwatanta shirin a matsayin gagarumar yaudara a duniya.

Shugabannin kasashe da dama za su hallara a taron MDD

Trump ya ce yana son abokan hulda na Amurka su dauki irin wadannan matakan domin matsa lamba ga Putin.