1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump ya halarci taron 'yan Kiripto a Amurka

July 28, 2024

Trump ya ce 'yan Kiripto su sha kuruminsu da zarar ya yi nasara a zaben watan Nuwambar da ke tafe, za a daina kuntata musu tare da mayar da sana'arsu karbabbiya kamar sauran sana'o'i.

Hoto: Kevin Wurm/REUTERS

Dan takarar shugabancin Amurka a jam'iyyar adawa ta Republican Donald Trump ya yi alkawarin idan har ya ci zabe zai tallata amfani da kudin badini na 'cryptocurrency' a kasar, yana mai cewa burinsa shi ne sanya Amurka a karkashin mulkinsa zama babbar mai amfani da kudaden''bitcoin'' da ake amfani da su a hada-hadar Kiripto.

Tsohon shugaban na Amurka da ke son dawowa mulki a karo na biyu ya fadi haka ne a yayin da ya halarci wani babban taro na 'yan Kiripto da aka yi jihar Tennessee a ranar Asabar.

Ya ce zai kafa majalisa ta musamman da za ta rika ba shi shawara kan harkoki da hada-hadar Kiripto a Amurka.

Shirin Dandalin Matasa

This browser does not support the audio element.

A cikin jawabin da ya kwashe sa'a guda yana yi wa 'yan Kiripton, ya yi kokarin kwatanta tsare-tsarensa kan bunkasa kudaden Kiripto da na gwamnatin Joe Biden wadda ya zarga da karya 'yan Kiripton, yana mai cewa burinsa shi ne 'a haki Kiripton a Amurka, sannan a sarrafa shi kuma ya zama kudi a Amurka'.