1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Trump ya jingine aikin rakiyar jiragen ruwa a Hormuz

May 6, 2026

Matakin na shugaban Amurka na zuwa ne bayan da aka fara samun arangama a mashigin Hormuz biyo bayan turjiya daga dakarun Iran.

Jiragen ruwa a makale a mashigin Hormuz
Jiragen ruwa a makale a mashigin HormuzHoto: Amirhosein Khorgooi/ISNA/WANA/REUTERS

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da jingine aikin rakiya tare da ba da kariya ga jiragen ruwan kasuwanci a mashigin Hormuz wanda ya yi wa lakabi da ''Project Freedom'', da nufin ba da damar cimma daidaito da hukumomin Iran.

A lokacin da yake sanar da hakan a shafinsa na Truth Social, Trump ya ce ya dauki wannan mataki ne bayan nasorin soji da Amurka ke samu a kan Iran, da kuma ci gaban da ake samu a tattaunawar da ake yi bisa shiga tsakanin Pakistan.

Artabu a Mashigin Hormuz

Sai dai shugaban na Amurka ya jaddada cewa takunkumin toshe tashoshin jiragen ruwan Iran da Amurka ta fara aiwatarwa tun a anar 13 ga watan Afrilu da ya gabata na nan daram.

A gefe guda kuma sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio, ya bayyana cewa Amurka ta kawo karshe kai hare-haren soji a kan Iran, amma kuma dakarun Washington na a shiye domin komawa fagen daga idan bukata ta kama.

Hoto: Iranian Foreign Minister/Telegram/AP Photo/picture alliance

Araghchi na ziyara a China

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi, ya gana a ranar Larabar da takwaransa na China Wang Yi a birnin Beijing, a daidai lokacin da rikici ke ci gaba da kamari a yakin Gabas ta Tsakiya.

Sai dai kamfani dillancin labaran China da ya ruwaito labarin ba yi karin bayani kan abubuwan da jamai'an diflomasiyyan suka tattauna a kai ba, a yayin da ake ci gaba da zaman dar-dar tsakanin Iran da Amurka, kuma kwanaki kadan kafin ziyarar da ake sa ran shugaba Donald Trump zai kai China a tsakiyar watan nan na Mayu.

Mashigin Hormuz mai abu ya rantse marar abu ya rantse

Gabanin ziyara ta Araghchi, an ruwaito sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio na kiran China da ta matsa lamba ga Iran domin bude mashigin Hormuz mai matukar muhimmanci ga tattalin arzikin duniya.

China dai na matukar cin moriyar mashigin na Hormuz, domin fiye da rabin adadin man fetur da kasar ke shigarwa na fitowa ne daga Gabas ta Tsakiya kuma yana bi ta wannan hanya.