Trump ya kai ziyarar ba zata kasar Iraqi
December 27, 2018Talla
Ziyarar dai na zuwa ne 'yan kwanaki bayan da ya sanar da janye sojojin Amirka daga Siriya mai makwabtaka da Iraqin.
Trump ya yi amfani da ziyarar wajen kare matsayinsa na janye sojojin Amirka daga Siriya matakin da ke shan suka daga bangarori da dama, yana cewa zaman sojojin a Siriya ba zama ne na dundundun ba. A saboda haka sojojin za su dawo gida.
'Yan majalisar dokoki na jam'iyyar Demokrat da Republican sun soki lamirin manufofinsa kan Siriya da cewa da sauran rina a kaba a yaki da 'yan IS.
A hanyarsa ta komawa gida Trump ya yada zango a sansanin sojin sama na Ramstein a Jamus inda ya gana tare da yin musabiha da wasu sojojin Amirka kafin ya wuce zuwa Washington.