1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Corona ta kama Trump da mai dakinsa

October 2, 2020

Shugaban Amirka Donald Trump da shi da mai dakinsa Melania Trump sun kamu da coronavirus. Shugaban ne ya tabbatar da haka a safiyar wannan Jumma'a.

USA Washington Donald Trump und Melania
Hoto: Andrew Caballerro-Reynolds/AFP/Getty Images

Sakamakon corona na  Trump din na zuwa ne 'yan awanni bayan likitoci sun sanar da cewa sun samu wani makusancinsa da corona.


 'Yan jarida sun ce sun ga Mr Trump a ranar Alhamis kuma bai nuna alamun rashin lafiya ba. Sai dai kuma likitoci na nuna damuwa ganin shugaban nada shekaru 74 musamman la'akari da cewa corona tafi yi wa masu yawan shekaru illa. Kamuwar da Trump ya yi da corona na zuwa ne wata guda gabanin zaben shugaban kasa wanda ya son yin tazarce a shugabancin na Amirka.