Trump ya nisanta kansa da kutsen majalisa
January 14, 2021![US-Präsident Donald Trump](https://static.dw.com/image/56165884_800.webp)
Da yake magana jim kadan bayan majalisar wakilan kasar ta sanar da tsige shi daga madafun iko, Trump ya ce babu wani wanda ya fi karfin doka a Amirka, yana mai ikirarin cewa masoyinsa na zahiri ba zai aikata irin wannan ba. Ya sha alwashin sai an hukunta duk mutanen da suka yi kutsen.
A jawabin da Trump din dai ya yi bai tabo batun tsige shi da majalisar wakilan kasar ta yi a ranar Laraba da daddare ba, amma tun da farko ya bayyana yunkurin a matsayin ci gaba da yi masa zagon kasa.
A yanzu za a mika kudurin tsige shi din zuwa majalisar dattawan kasar wace za ta tabbatar, sai dai kuma ana zullumin dattawan ba za su iya yin wannan aiki a cikin 'yan kwanakin da suka rage wa Trump ya kammala wa'adi sa ba. A makon gobe ne dai za a rantsar da Joe Biden a matsayin sabon shugaban na Amirka.