1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Trump ya kori mai ba shi Shawara kan Tsaro

May 2, 2025

Shugaban na Amurka Donald Trump ya ce zai nada korarren jami'in nasa a matsayin Jakadan Majalisar Dinkin Duniya.

Mike Waltz zai zama sabon Jakadan Amurka a Majalisar Dinkin Duniya
Mike Waltz zai zama sabon Jakadan Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Hoto: Andrew Leyden/NurPhoto/picture alliance

Shugaban Amurka Donald Trump ya kori mai ba shi Shawara kan al'muran Tsaro  Mike Waltz, biyo bayan badakalar bullar bayanan yadda aka tsara kaddamar da hare-hare a kan Yamen.

Trump ya ce zai bai wa mista Waltz sabon mukamin Jakadan Amurka a Majalisar Dinkin Duniya bayan sauke shi daga mukamin da ya ke kai.

Mike Waltz zai ajiye mukaminsa

Wannan shi ne karon farko da Trump ya yi wa jami'an gwamnatinsa garambawul, kuma ya ce a yanzu Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ne zai maye gurbin Waltz a matsayin mukaddashi.

Shugaba Trump ya kuma yaba da aikin da Waltz ya yi, inda ya ce lokutan da ya shafe a fagen daga da Majalisar Dokokin Amurka da kuma mukamin da ya bashi, Waltz din ya yi aiki tukuru don tabbatar da manufofin kasarsa.

Na yi abinda ba a taba yi ba a kwanaki 100 - Trump

To sai dai kuma tun bayan bullar bayanan sirrin na yadda Amurka ke kitsa kai hari kan Yemen, mista Waltz din ke dari-dari da kuma nuna sanyin jiki a yadda ya ke gudanar da al'amuransa.