1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Trump ya kosa da yaki da Iran

Suleiman Babayo ZMA
June 10, 2026

Shugaban Amurka ya harzika kan yadda Iran take jan kafa na tattauna yarjejeniyar zaman lafiya.

Shugaba Donald ⁠Trump na Amurka
Shugaba Donald ⁠Trump na AmurkaHoto: Samuel Corum/CNP/ZUMA/IMAGO

Shugaba Donald ⁠Trump na Amurka ya bayyana cewa Iran tana bata lokacin wajen tattaunawa kan samun zaman lafiya, kuma kasar ta Iran za ta fuskanci sakamakon abin da take aikatawa.

Lamura sun kakare

Shugaba Trump wanda ya wallafa haka a shafinsa na sada zumunta, bai yi wani karin haske ba, bisa abin da yake nufi.

Jiragen yakin Amurka da ke Gabas ta TsakiyaHoto: MCSN Dan Snow/Navy Office of Information/dpa/picture alliance

Amma wannan ya zama manuniya da kosawa da ya yi kan samun yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin bangarorin biyu.

Kalaman na Shugaban Amurka suna zuwa bayan kasashen biyu sun sake yin musanyen wuta, inda Amurka ta kai hare-haren bayan wani hari kan jirginta mai saukan ungulu, ita kuma Iran ta mayar da wuta kan kasashen yankin da suke da sansanonin sojan Amurka.