1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump ya lashe zaben fidda gwani a Iowa

Mouhamadou Awal Balarabe
February 4, 2020

Shugaba mai ci a yanzu a Amirka Donald Trump ya samu rinjaye a kan abokan hammayarsa biyu a zaben farko na fidda dan takara a jam’iyyar Republican a jihar Iowa.

USA Präsident Donald Trump
Hoto: Imago Images/Zumapress/B. Cahn

Kamar yadda aka yi hasashe tun da farko, shugaban Amirka Donald Trump ya lashe zaben farko ne neman takara karkashin jam'iyyarsa ta Republican. A jihar Iowa da ke zama zango na farko, Trump ya yi nasara a kan abokan takara biyu, inda ya samu rinjayen kuri'u a gaban tsohon gwamnan Massachusetts Bill Weld da kuma ma'aikacin rediyo Joe Walsh wadanda suka samu sama da kashi daya cikin dari na kuri'un.

Tuni dai aka tabbatar cewa Donald Trump zai tsaya takarar shugaban kasa a ranar 3 ga Nuwamba saboda jihohi da dama na Amirka sun soke zaben fidda gwani da suka shirya karkashin jam'iyyar Republican.

A daya bangaren ma, jam'iyyar adawa ta Democrat na gudanar da zaben fidda gwani a jihar ta Iowa, inda nan gaba kadan za a san mutumin da ya samu nasara tsakanin 'yan takaran, a matakin farko na neman mutumin da zai jaroranci jam'iyyar yayin zaben kasa baki a kasar ta Amirka a watan Nuwamba da ke tafe.