1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Ana tuhumar Trump kan zargin bayar da toshiya

Ramatu Garba Baba
April 5, 2023

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya musanta tuhume-tuhumen aikata wasu manyan laifuka da wata kotun gundumar birnin New York ta gabatar masa.

Trump a kofar shiga kotun da ke birnin New York
Trump a kofar shiga kotun da ke birnin New York Hoto: Mary Altaffer/AP Photo/picture alliance

A yayin gajeren zaman da kotun gundumar ta yi a birnin New York, wanda shi ne irinsa na farko cikin tarihin Amurka, da aka taba kai wani tsoho ko shugaba da ke mulki, mai gabatar da kara Alvin Bragg ya baiyana cewa, galibin wadannan laifuka suna da nasaba da karerayi da zamba da ake zargin Donald Trump ya tafka a cikin harkokin kasuwancinsa da kuma yadda ya biya Stormy Daniels, wata da ta yi kaurin suna wajen fina-finan batsa, domin kada ta fallasa harkar da suka yi da Trump kafin zaben shekarar 2016 da ya yi galaba.

Batun gurfanar da Mista Trump ya janyo rabuwar kawuna, yayin da bangaren shigar da kara suka lashi takobin tabbatar da zargin da ake yi wa tsohon shugaban, masu kare shi, sun yi watsi da karar suna masu cewa, bita da kullin siyasa ne, ganin ya aikata wadannan laifukan tun kafin ya zama shugaban kasa.