Trump ya nada Tillerson sakataren harkokin waje
December 13, 2016A wata sanarwa da ya fitar Donald Trump ya bayyana cewa Rex Tillerson dan shekaru 64 da kuma ke da alaka ta kut da kut da Shugaba Vladmir Putin na Rasha zai mayar da hankali ne da farko ga farfado da kuma inganta huldar diplomasiyyar kasar ta Amirka da ta Rasha wacce ta sukurkurce a sakamakkon mamayar yankin Krimiya da kuma yakin kasar Siriya.
Mista Trump dai ya bayyana sakataren harkokin wajen gwamnatin tasa a matsayin mutumin da ya san makamar aikin tafiyar da harkokin duniya da kuma ke da alaka da shugabannin kasashen duniya da dama.
Sai dai ana ganin dangantakar Mista Tillerson da kasar Rasha na iya haifar masa da kalubale a lokacin tabbatar da nadin nasa a nan gaba a gaban majalisar dattawan Amirka, musamman ganin irin yadda hukumar leken asirin kasar ta Amirka ta zargi Rasha da yin kutse cikin harkokin zaben kasar wanda Donald Trump din ya lashe.