1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Amirka: Trump na tunanin sake tsayawa takara

March 1, 2021

Tsohon Shugaban kasar Amirka Donald Trump ya yi jawabi na farko tun bayan saukarsa daga mulkin kasar a watan Janairu.

USA Florida | US-Republikanertreffen CPAC| Donald Trump Rede
Hoto: Octavio Jones/REUTERS

A yayin jawabinsa na ranar Lahadi a wurin taron shugabannin siyasa masu ra'ayin rikau na shekara shekara, ya fara yi wa mahalarta taron tambayar cewa sun fara begen salon mulkinsa ko? Daga nan sai ya dora da ci gaba da sukar gwamnatin Joe Biden, ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba.


 ''Watan farko na mulkin Joe Biden ya kasance mai hatsari da wani shugaba ya taba yi a wannan zamani. Gwamnatin Biden tuni ta nuna cewa ba ta son samarwa da jama'a ayyukanyi ba kuma ta san kare martabar iyalai da iyakoki da kuma makamashi kuma Biden bai son ci gaban mata da kimiyya.'' in ji Trump 


Donald Trump ya kara da cewa ba shi da muradin sake kafa wata sabuwar jam'iyya kamar yadda ake ta jita-jita a kai, yana mai ikirarin cewa watakila ma ya sake tsayawa takara a 2024 kuma ya kayar da jam'iyyar Democrat a karo na uku, wato ke nan har yanzu bai saduda cewa an kada shi a zaben shekarar da ta gabata ba a kasar ta Amirka.