1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaVenezuela

Trump ya nuna aniyar tattaunawa da Maduro

November 18, 2025

Ko da yake shugaban Amurka Donald Trump ya ce zai tattauna da Nicolas Maduro, bai fidda tsammanin tura sojoji zuwa kasar ba.

Shugaban Amurka Donald Trump da shugaba Maduro na Venezuela
Shugaban Amurka Donald Trump da shugaba Maduro na VenezuelaHoto: Evan Vucci/AP/dpa/Cristian Hernandez/AP/picture alliance

Shugaban Amurka Donald Trump a ranar litanin ya ce a shirye yake ya tattauna da shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro, amma bai yi watsi da tura sojojin Amurka zuwa Venezuela din ba.

A wani lokaci zan tattuna da shi inji Trump a lokacin da ya ke amsa tambayoyin manema labarai a ofishinsa.

Da aka tambaye shi ko zai yi watsi da aika sojojin Amurka zuwa Venezueala, Trump ya ce a'a ba zan yi watsi da hakan ba, ba zan watsi da komai ba.

Ya kamata mu kula da Venezuela  kawai, ya kara da cewa sun watsar da dubban mutane daga gidajen yarin su cikin kasarmu.

'Yan sa'o'i kadan shugaba Maduro a wata tattaunawa da ake yi da shi a gidan Talabijin duk mako ya ce a shirye yake a tattauna da shi gaba da gaba.

"Wannan kasa za ta ci gaba da samun zaman lafiya, a Amurka duk wanda ke son tattaunawa da Venenzuela zai tattauna da ita gaba da gaba, ba  tare da wata matsala ba inji maduro''.