Trump ya fitar da Amurka daga kungiyoyin duniya 66
January 8, 2026
Shugaba Donald Trump ya ce matakin gwamnatinsa na janye Amurka daga kungiyoyin duniya, ya biyo bayan la'akari da ba su biyan bukatun kasarsa, ya umurci dakatar da duk wani tallaafin kudade ga kungiyoyin cikin gaggawa ciki har da hukumomin Majalisar Dinkin Duniya 31 da wasu kungiyoyi 35 wadanda ba na Majalisar Dinkin Duniya ba.
Fadar White House ta ce kungiyoyin suna gudanar da ayyukan da suka sabawa muradun Amurka na tsaro da wadatar tattalin arziki da kuma 'yancinta. "Ko ba komai, Amurka ta fice daga kungiyoyi masu adawa da ita kuma marasa amfani wadanda ake almubazzarancin kudi." inji Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio. Ya kara da cewa "Ana ci gaba da nazari kan wasu kungiyoyin da za a raba gari da su nan gaba." Yawancin kungiyoyin da matakin ya shafa suna aiki a fannoni kamar muhalli da manufofin yanayi ko daidaiton jinsi.
Matakin Trump na raba gari da kungiyoyin bai fayyace adadin kudaden da gwamnatin za ta yi tsiminsu ba. Tun da ya koma kan karagar mulki wa'adi na biyu, Trump ya matsa kaimi wajen fitar da Amurka daga wasu tsare-tsare na kasa da kasa, da suka hada da hukumar lafiya ta duniya da hukumar al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO.
A wa'adinsa na biyu kuma, Trump ya dakatar da tallafin Amurka ke ba wa kasashen duniya da dama ciki har da Afirka, ya kuma katse ayyukan kungiyoyi da wasu hukumomi wanddanda ya ce ba su da amfani.