Amurka da China sun sasanta rikicin kasuwanci
October 30, 2025
Ganawar wanda shi ne karo na farko da shugabannin kasashen biyu suka yi hadu da juna tun bayan komawar Trump kan karagar mulki kawo na biyu, ya samar da abin da bangarorin biyu suka kira "daidaita dabaru" a dangantakarsu, wanda aka kulla kan yarjejeniyar fitar da kaya zuwa Amurka da kuma rage harajin Amurka da kashi 47 cikin 100 daga 57 cikin 100 kan kayayyakin da China ke shigowa da su kasar.
Shugaba Trump ya bayyana a yayin wani taron manema labarai cewa, "Mun dawo da kasar Sin kan teburin tattaunawa, za su sayi kayanmu, mu kuma za mu rage haraji, kuma duniya na kallon dawowar zaman lafiya."
China ta amince da dakatar da sabbin takunkumin hana fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje na tsawon shekara guda - matakin da zai kawar da rikicin da ke kunno kai ga masana'antun da suka dogara da kayayyakin, daga motocin lantarki zuwa tsarin tsaro.
Yarjejeniyar ta biyo bayan gargadin da aka shafe watanni ana yi cewa tsaurara matakan China, na iya kawo cikas ga masana'antun duniya da kuma kara tsadar kayayyaki a kasuwannin yammacin duniya. Trump ya yaba da yarjejeniyar a matsayin "babban ci gaba," kodayake manazarta sun lura cewa na wucin gadi ne.
Gabannin zantawar shugabannin biyu na tsawon sa'a 1 da mintuna 40, akwai mumunar sabanin tsakanin shugabannin kan batutuwan da suka hada da haraji mai tsaruri kan kayan fito da China ke shigarwa Amurka kamar naurorin kwamfuta da wayar salula da sauran albarkatu.