1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump ya sake kalubalantar NATO a kan kudaden tsaro

January 8, 2025

Zababben shugaban kasar Amurka Donald Trump, ya sake yin kira ga kasashe mambobin kungiyar kawancen tsaro ta NATO da su kara kudadensu na tsaro, yana mai nuna cewa har yanzu ba sa ba da kasonsu yadda ya dace.

Zababben shugaban Amurka, Donald Trump
Zababben shugaban Amurka, Donald TrumpHoto: Andrea Renault/STAR MAX/picture alliance

Da yake jawabi lokacin wani taron manema labarai a wajen shakawarsa na Mar-a-Lago a jiya Talata, zababben shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ce ya kamata kasashen na NATO su rika bayar da kaso 5% na kudadensu na shiga a fannin tsaron, akasin kashi 2% da suke bayarwa a yanzu.

Zababben shugaban na Amurka wanda ya sha sukar kungiyar kawancen tsaron kasashen yammacin duniyar a mulkinsa na farko a Amurkar, ya ce dukkkaninsu za su iya samar da wadannan kudaden.

A bara ne dai kasashen na NATO suka ce za su rika bayar da kaso biyu cikin 100n ga harkokin tsaro, to sai dai sabon shugaban kungiyar Mark Rutte shi ma yana da ra'ayi tare da nuna dacewar kara kudaden da ake samarwa.