Amurka da Indiya sun kulla yarjejeniyar kasuwanci
February 3, 2026
Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cimma yarjejeniyar kasuwanci da kasar Indiya, bayan shafe watanni ana ja-in-ja a tsakanin Washington da New Delhi da ke zama na daya daga cikin jerin kasashen da tattalin arzikinsu ke bunkasa cikin hanzari a duniya.
Trump ya kuma ce firaministan Indiya Narendra Modi ya amince ya dakatar da sayen man Rasha tare da yin alkawarin rubanya yawan man da Indiya ke saya daga Amurka musamman man Venezuela da ke karkashin ikon Washington.
Har ila yau, shugaban na Amurka ya ce za a sassauta harajin kwaston kan kayayyakin Indiya zuwa kashi 18% wanda a halin yanzu ke a tsakanin kashi 25% zuwa kashi 50%.
Wannan yarjejeniya za ta fara aiki ne take-yanke domin kawo karshen yakin kasuwanci da Washington da New Delhi suka shafe watanni suna yi, tun bayan sake dawowar Trump kan karagar mulki.