1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump ya fara daukar matakan sauya ayyukan Obama.

January 21, 2017

Sabon shugaban Amirka Donald Trump ya fara wa’adin mulkinsa tare da sanya hannu akan wasu matakai na sauya ayyukan wanda ya gabace shi yayin da yake cigaba da fuskantar zanga zangar adawa a ciki da wajen kasar.


Washington Amtseinführung Trump
Hoto: Picture-Alliance/AP Photo/E. Vucci

Sabon shugaban Amirka Donald Trump ya fara wa’adin mulkinsa tare da sanya hannu akan wasu matakai na sauya ayyukan wanda ya gabace shi. Darewarsa karagar mulki ya fara cin karo da zanga zangar adawa a cikin kasar da kuma kasashen waje.

Sabon shugaban kasar ta Amirka Donald Trump a ranar Juma’a ya rattaba hannu akan wata doka wadda ke zama matakin farko na sauya shirin lafiya na shugaban day a gada Barack Obama yan sa’oi bayan da ya yi rantsuwar kama aiki.

Hoto: Reuters/C. Barria

Trump wanda ya yi alkawura da dama a lokacin yakin neman zabe na soke shirin lafiyar da galibin al’umma za su iya samu wanda aka yiwa lakabi da Obamacare.  Dokar wadda ya sanyawa hannu musamman za  ta shafi muhimmin bigire na tsarin lafiyar wanda ya bukaci kowa ya mallaki Inshorar lafiya ko kuma ya fuskanci tara.

Hoto: Getty Images/A. Wong

Wannan bangare dai wanda ya bada dama ga kowa ya mallaki inshora, masu harkar inshorar na ganin cewa ya bada kafa ga mutanen da basu da inshora su ci moriyar harkar lafiyar.

Shugaba Donald Trump ya gaji tsohon shugaba Barack Obama,wanda kuma a cikin jawabin da ya yi ya ce zai sake dawo da ayyuka da daraja da kuma martaba da Amirkan ta rasa a tsawon lokaci da dama, sannan ya ce zai tsare iyakokin Amirkar. 

Hoto: picture-alliance/AP Photo/T. Ireland

Tun da fari dai sai da 'yan sanda suka yi amfani da barkonon tsohuwa don tarwatsa masu zanga-zanga a birnin Washington inda masu zanga zangar suka rika jifa da duwatsu tare da farfasa tagogi, gabannin rantsar da sabon shugaba Donald Trump.

Yayin da shugaba Trump da magoya bayansa da ma wasu tsoffin shugabannin kasar gami da wasu manyan baki suka taru a harabar gudanar da bikin rantsuwar ne dai masu adawa da manufofin naTrump suka bi kusa da wajen, sai dai jami'an tsaro sun tarwatsa su.