Shirye shirye sun kankama domin rantsar da Trump
January 19, 2017Talla
A gobe Juma'a ne za a rantsar da zabbaben shugaban kasar Amurka Donald Trump a matsayin shugaba na 45.
Tuni dai Trump ya sauka a birnin washinton cike da kudirin canza siyasar kasar a cikin shekaru hudu.
Tun da farko sai da ya wallafa a shafinsa na Twitter yana mai cewa ''Na dauki aniyar fara aiki tukuru domin al'ummar kasar Amurka''
Za a yada bikin rantsuwar kai tsaye ta a kafafen yada labarai a duniya. Da zarar an rantsar da shi Trump zai sa hannu a wasu dokoki hudu ko biyar wadanda suka hada da bangaren muhalli da shige da fice da kuma kwadago tare da yin watsi da duk wani tsari da yake ganin bai yi daidai da manufofinsa ba, ba tare da sahalewar majalisa dokoki ba.