1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump ya sha sukar 'yan siyasa a COP23

Yusuf Bala Nayaya
November 11, 2017

Sanatoci biyar daga Amirka sun bayyana cewa har yanzu Amirka na da rawar takawa a fagen yaki da sauyin yanayi duk da shirin Shugaba Donald Trump na ficewa daga yarjejeniyar sauyin yanayi ta birnin Paris.

COP23 | AL Gore auf der Weltklimakonferenz in Bonn
Hoto: picture-alliance/dpa/H. Kaiser

A cewar Sanata Ben Cardin, daga  Maryland matsalar sauyin yanayi barazana ce ga tsaron kasar ta Amirka:

"Sauyin yanayi abu ne da ke da muhimmanci mu tashi tsaye mu kawar da shi don tsaron kasarmu, mun ji ba sau daya ba sau biyu ba daga jami'an sojin Amirka. Akwai 'yan gudun hijira saboda matsala ta sauyin yanayi ta haddasa rikici a kasashe, duk wadannan na daga cikin abin da muke kallo a matsayin barazana ga tsaron Amirka."

Sanatocin daga jam'iyyar Democrats sun bayyana haka ne a ranar ta Asabar a wurin taron sauyin yanayi na duniya COP23 da ke wakana a nan birnin Bonn. Shi ma dai  AL Gore tsohon mataimakin shugaba a Amirka ya ce suna fatan jan hankali na Trump ya sauya matsaya. Yayin da a bangare guda kuma wasu dubban al'umma masu rajin kare muhalli suka gudanar da zanga-zanga ta kalubalantar mahukunta kan kare muhalli, wacce a lokacin ta a ka zagaya da mutum-mutumi na Shugaba Trump ana kalubalantarsa.