SiyasaArewacin Amurka
Trump ya soke ayyukan hukumar bunkasa ci gaba a Afirka MCC
April 24, 2025
Talla
Shugaba Donald Trump na Amurka ya bada umarnin dakatar da ayyukan hukumar da ke bunkasa ci gaba da zuba jari ta Millennium Challenge Corporation (MCC) ba tare da bata lokaci ba, duk da cewa Amurka za ta karasa wasu ayyukan hukumar na biliyoyin daloli a kasashen Côte d'Ivoire da Mongolia da Nepal da kuma Senegal.
Karin bayani: Amurka ta soke kashi 83 na ayyukan USAID:
Matakin Trump na zuwa a daidai lokacin da shugaban kasar Zambia Hakainde Hichilema ya rattaba hannu da hukumar ta MCC wajen samar da ababan more rayuwa a kasar ciki har da aikin samar da wutar lantarki da bunkasa noman rani da kuma gina manyan tituna.