1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump ya soke duk manufofin gwamnatin Joe Biden

Aliyu Abdullahi Imam
November 29, 2025

Shugaban na Amurka ya ce kashi 92 cikin 100 na manufofin da tsohon shugabann kasar ya zartar sun saba doka, yana zargin an yi amfani da naurar kwaikwayon sa hannu wato 'autopen'

USA Washington D.C. 2025 | Marco Rubio flüstert Donald Trump während Antifa-Rundtisch zu
Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio da Shugaba Donald TrumpHoto: Jim Watson/AFP

Shugaban Amurka Donald Trump ya sha alwashin soke duk wasu manufofin tsohuwar gwamnatin jam'iyyar Democrat karkashin Joe Biden, yana zargin Biden ya yi amfani da sa hannu kan wasu manufofi da 'autopen' naurar kwaikwayon sa hannu kan wasu tsare-tsaren gwamnati.

A cikin wani sako da ya wallafa Intanet, Trump ya sanar da soke kashi 92 cikin 100 na umrnin da Joe ya amince da su a gwamnatinsa ciki har da batun baki da yarjejeniyar muhalli da kuma dai-daito da batun ma'aikata.

Wannan dai na zuwa ne yayin da Trump ya dakatar da duk wani yunkuri na masu neman mafaka a Amurka, bayan da wani dan kasar Afganistan ya kashe wata jami'ar tsaron kasar guda daya tare da raunata wani a babban birnin kasar. Matakin ya sa hukumomin Amurka fara nazari kan masu katin zama na wucin gadi 'green cads' da aka baiwa wasu mutane daga kasashe 19.

Gwamnati ta kuma dakatar da duk wasu shirye-shirye na tsugunar da 'yan kasar Afganistan a kasar tare da fara nazarin wadanda aka ba wa izinin zama a karkashin gwamnatin Biden da ta gabata.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta kuma dakatar da bayar da biza ga mutanen da ke rike da fasfo din Afghanistan, in ji sakataren harkokin wajen kasar Marco Rubio.