1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Trump ya tattauna ta waya da Xi Jinping

September 20, 2025

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Washington da Beijing na kusa da cimma yarjejeniya dangane da Tik Tok, sannan kuma zai kai ziyara China bayan ya tattaunawa ta waya da takwaransa Xi Jinping.

Shugaba Donald Trump da takwaransa Xi Jinping
Shugaba Donald Trump da takwaransa Xi JinpingHoto: Susan Walsh/AP/picture alliance

Jim kadan bayan tattaunawar da shugabannin biyu suka yi a ranar Juma'a, shugaban Amurka Donald Trump ya wallafa sako a shafinsa na Truth Social, inda ya ce sun yi musayar yawu da Xi Jinping kan muhimman batutuwa da dama ciki har da kasuwanci da samar da yarjejeniya dangane da shafin Tik Tok da kuma bukatar kawo karshen yakin Rasha da Ukraine.

Karin bayani: Trump ya ce ya saka hannu kan dokar da za ta tsawaita dakatar da haraji kan kasar China

Sai dai kamfanin dillacin labarai mallakin gwamnatin China ya ruwaito cewa shugaba Xi Jinping ya bukaci Donald Trump da ya kaucewa yin gaban kansa wajen kakaba harajai da ke kawo tarnaki ga harkokin kasuwanci a duniya.

Shugabannin biyu sun amince su yi ganawar keke da keke a daura da taron koli na kungiyar kasuwaci ta kasashen nahiyar Asiya APEC, wanda za a gudanar daga ranar 31 ga watan Oktoba zuwa ranar daya ga watan Satumban 2025 a Koriya ta Kudu.