Trump ya tsawaita wa'adin da ya bai wa Iran da sa'o'i 24
April 5, 2026
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya fada a ranar Lahadi cewa ya ƙara wa’adin da ya bai wa Iran da sa’o’i 24 domin ta cimma yarjejeniya ta buɗe mashigar Hormuz, ko kuma ta fuskanci munanan hare-hare kan muhimman wurarenta na makamashi.
Trump ya wallafa a shafinsa na Truth Social cewa "kuna da nan da zuwa Talata, ƙarfe 8:00 na yamma agogon Gabashin Amurka!”
Trump: Za mu iya daina kai hari Iran nan da makonni 2-3
Sabon wa’adin, wanda ya yi daidai da ƙarfe 0000 agogon GMT na ranar Laraba, na nufin Iran za ta samu ƙarin yini guda a wa'adin Trump na farko domin ta amince a daidaita, ko kuma ta fuskanci barazanar lalata tashoshin wutar lantarki da gidajenta.
Tun bayan fara hare-haren bamabamai da Amurka da Isra’ila suka kaddamar a ranar 28 ga Fabrairu, Iran ta toshe mashigar ruwa ta Hormuz, wadda ke da matuƙar muhimmanci ga zirga-zirgar mai da iskar gas a duniya.
Trump ya jinkirta kai wa cibiyoyin lantarkin Iran hari
Iran ta ce ko a jikinta da barazanar Trump, kuma ana taba mata tashoshin lantarki to gaba daya na Gabas ta Tsakiya za su durkushe.