1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump ya tura dakaru ko da ta baci a Kwango

Yusuf Bala Nayaya
January 5, 2019

Donald Trump ya tura dakarun sojoji 80 zuwa Gabon ta yadda za su zauna cikin shirin ko ta kwana, idan an samu barkewar rikici a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango bayan zaben da kasar ta yi mai cike da takaddama a cikinsa.

Deutschland US-Army: Übergabe der Hubschrauberstaffeln in Illesheim
Hoto: picture-alliance/dpa/N. Armer

A wata wasika da ya tura zuwa ga majalisa, Shugaba Trump ya ce ya dau wannan mataki na tura dakarun sojan na Amirka ne saboda su zauna cikin shiri ko da zanga-zanga za ta balle a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango biyo bayan zaben da aka yi a ranar 30 ga watan Disamba da ya gabata.

Dakarun tare da jirgin soja za su taimaka idan bukatar hakan ta shi wajen kwashe 'yan kasar ta Amirka da jami'an diflomasiya na Amirka da ke zaune a birnin na Kinshasa.

Zaben dai da aka yi a wannan kasa ta  Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da ake sa rai zai samar da kafa ta kawar da gwamnatin Shugaba Joseph Kabila, an yi zargi na samun kura-kurai da tsaiko wajen fitar sakamako, abin da ke zama barazana ga kasar da ta yi kaurin suna wajen tashe-tashen hankula.