Trump zai ba wa Ukraine karin makamai
July 8, 2025
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi mi'ara koma baya inda a daren jiya Litinin ya fadi cewa zai aike wa Ukraine da karin makamai, bayan da a makon da ya shige fadar mulki ta White House ta sanar da katse tallafin kayan yaki da take bai Kiev.
Trump ya ce la'akari da munanen hare-hare masu zafi da Rasha da kai mata a baya-bayan nan, dole ne Amurka ta aike wa Ukraine da karin makamai musamman ma na kare kanta, sannan kuma ya bayyana rashin jin dadindsa a game da aniyar shugaba Putin.
Karin bayani: Trump ya zargi Rasha da kin kawo kashen yakin Ukraine
Har kawo wannan lokaci mahukuntan Ukraine ba su yi martani a game da wannan mataki ba, amma a safiyar Talatar nan rundunar tsaron kasar ta ba da tabbacin dakile wani hari da Rasha ta yi yunkurin kai wa da jirage marasa matuka a yankunan Soumy da Kharkiv.
Karin bayani:'Putin na Rasha ba zai hakura da manufofinsa a Ukraine ba'
Tun a watan Janairu da ya gabata ne dai shugaban na Amurka Donald Trump ke kara kusantar takwaransa na Rasha Vladimir Putin tare da yi masa matsin lamba don kawo karshen yakin Ukraine, sai dai har kawo wannan lokaci haka ba ta kai ga cimma ruwa ba.