Trump ya yi barazanar kaddamar wa Najeriya hari
November 2, 2025
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar daukar matakin soji a kan Najeriya, muddin kasar da ta fi kowace yawan al'umma a nahiyar Afirka ba ta dakatar da abin da ya kira 'kisan kare dangi da 'yan ta'adda masu kaifin kishin Islama ke yi wa Kiristoci ba', zargin da fadar mulki ta Abuja ta yi watsi da shi.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Truth Social da tsakiyar daren ranar Asabar, Donald Trump ya ce Amurka za ta dakatar da dukkan tallafin da take bai wa Najeriya nan take idan har gwamnati ta ci gaba da nuna halin ko in kula kan kisan da ake yi wa mabiya addinin Kirista a kasar.
Hakazalika shugaba Trump ya ce Amurka na iya kutsawa Najeriya da karfin soji domin kakkabe 'yan ta'adda masu aikata ta'asa da sunan addinin Islama, sannan ya umurci ma'aikatar yaki ta Amurka da ta shirya domin yiwuwar kai wa Najeriya samame.
Karin bayani: Trump ya saka Najeriya a jerin kasashen da ake wa Kiristoci barazana
Wannan furici na Trump na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatinsa ta saka Najeriya a jerin kasashen da ake yi wa Kirista kisan kare dangi, zargin da fadar mulki ta Abuja ta musanta.