1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump ya yi barazanar kara haraji kan EU

Abdullahi Tanko Bala
December 20, 2024

Zababben shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump ya yi barazanar kakaba wa kasashen kungiyar tarayyar Turai karin haraji idan ba su kara yawan mai da Iskar da suke saye daga Amurka ba.

Donald Trump
Donald TrumpHoto: Brian Snyder/REUTERS

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Trump yace ya sanar da kungiyar tarayyar Turai cewa dole ne su kara azama wajen cike gibin cinikayyarsu da Amurka ta hanyar kara yawan mai da iskar Gas da suke saye daga Amurka.

A bisa alkaluman kididdiga na Amurka, kungiyar tarayyar Turai ita ce kan gaba wajen sayen makamashi daga Amurka.

Tuni dai Trump ya yi alkawarin lafta haraji mai yawa a kan wasu kasashe uku da ke kan gaba wajen cinikayya da Amurka wadanda suka hada da Canada da Mexico da kuma China idan ya karbi ragamar mulki a ranar 20 ga watan Janairun 2025

Matakin dai ka iya yin mummunan tasiri ga tattalin arzikin duniya.

Jamus ita ce kan gaba a cikin kasashen Turai da ke safarar kaya zuwa Amurka galibi motoci da na'urori da kuma magunguna.