Trump ya yi barazanar lalata cibiyoyin lantarkin Iran
March 22, 2026
Talla
Ana ganin barazanar Amurka na lalata cibiyoyin lantarkin Iran idan ba ta bude mashigin Hormuz ba a matsayin bude wani sabon babi na rikicin da ke shiga mako na hudu da fara shi. Sai dai Iran ta yi gargadin idan aka kai wa cibiyoyin lantarkinta hari, za ta mayar da martani ta hanyar lalata duk wasu kayan samar da makamashi na Amurka da Isra'ila da ke yankin.
Karin bayani: Amurka ta kai hari kan cibiyoyin nukiliyar Iran uku
Hakan na zuwa ne yayin da Iran din ta kai sabbin hare-hare Isra'ila, bayan da aka kai wa babbar tashar nukiliyarta ta Natanz da ke Tehran hari. Sai dai Isra'ila ta ce ba ita ta kai harin ba.